IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Kur’ani A Birnin Tubruk Na Kasar Libya

23:54 - July 13, 2015
Lambar Labari: 3327736
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar harda da kuma tajwidin kur’ani mai tsarki a birnin Tubruk na kasar Libya tare da halartar mahardata.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwasat cewa, Hussain Ali Alsaqir shugaban ofishin da ke daukar nauyin shirya gasar ya bayyana cewa, yanzu haka an fara gudanar da gasar harda da kuma tajwidin kur’ani mai tsarki a birnin Tubruk na kasar Libya tare da halartar mahardata 60 daga makarantu daban-daban na kur’ani.

Ya ci gaba da cewa wanann gasa tana daga cikin irinta da aka saba gudanarwa, amma a wannan karon an mayar da hankali ga harda da kuma kyautata karatun wato ilimin tajwidi, yayin da a lokutan baya a kan hada har da bangaren karatu baki daya.

A cikin makonni biyu da suka gabata ne aka gudanar da gasar wadda ta kebanci karatu zalla, inda aka samu halartar makaranta fiye da dari biyu daga sassa na kasar, da nufin kebance gasa ta gaba ta zama ta hard ace kawai da kuma lura da kiyaye ilimin kyautata karatun.

A lokacin bude gasar an samu halattar manyan jami’ai da suka hada da Abdulsalam Al-sharif shugaban ofishin harkokin addini na birnin, da kuma Annaji Maziq babban magajin garin birnin, sai kuma Abdunnabiyi daya daga cikin yan majalisar dokokin Tubruk, gami da wasu malamai da kuma fitattun mutane na wannan birni.

3327340

Abubuwan Da Ya Shafa: libya
captcha