Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na PNN cewa, jami’an yan sanda na haramtacciyar kasar Israila ta kara tsananta tsaro a cikin da wajen birnin Qods mai alfarma a cikin wadannan kwanaki na karshen watan Ramadan mai alfarma.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan mataki da yahudawan suke dauka yana da alaka ne da tsoron da yahudawan suke ciki dangane da batun tarukan ranar Qods wanda a ka yi a cikin wannan mako, inda har yanzu suke ci gaba da daukar wannan mataki.
Tun farkon watan nann dai aka fara hana mutane zuwa salla a masallacin mai alfarma, musamman ma wadanda a ba a cikin yankin gabacin birnin suke ba, inda ake hana su zuwa salla tare da tilasta su komawa zuwa yankunansu.
Haramtacciyar gwamnatin yahudawan tana yin amfani da karfin da ya wuce hankali wajen hana gudanar da salla a masalalci, ko da kuwa mutanen yankin ne takan kafa musu wasu sharudda, musamman dangane da shekaru.
3327574