Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gio na jaridar Al-ahram cewa, Ala Badr Sayyid Muhammad karamin yarto ne dan shekaru 10 da haihuwa da ya hardace dukkanin alkur’ani mai tsarki a kasar.
Wannan yaro ya halarci gasar kur’ani mai tsarki ta Alfath a yankin an Asyut, a nan kuma ya samu damar hardace dukkanin kur’ani bayan da ya samu damar bin abin da yake karantawa, kuma ya samu taimakon ubangiji kan hakan.
Atef Alazazi daya daga cikin manyan jami’ai na gungumar Asyut ya bayyana cewa, hardace dukkanin kur’ani mai tsarki cikin watanni uk wata babbar mu’jiza ce wadda kuma wannan karamin yaro Ala Badr Sayyid Muhammad dan kasar Masar ya nuna.
3328101