IQNA

Babban Mai Fatawa Na Quds Ya Gargadi Yahudawa Kan Gigin Taba Makabartar Musulmi

23:24 - July 16, 2015
Lambar Labari: 3328846
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Muhammad Hussain babban mai bayar da fatawa a birnin Quds ya gargadi yahudawan sahyuniya da su guji duk wani gigin da ka kai su gat aba makabartar musulmi a wannan birni.


Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palastine Online cewa, Sheikh Muhammad Hussain a jiya ya fitar da bayani da a cikinsa ya gargadi yahudawan sahyuniya da su guji duk wani gigin da ka kai su ga taba makabartar (Ma’amaninillah) mallakin musulmi a wannan birni na Quds. 

Rahotanni sun ce kwamitin majalisar haramtacciyar kasar Isra’ila ya amince da gida  gidaje dari da casein da biyu da kuma otel mai dakuna dari da tamanin a cikin wata makabratr musulmi mai tsohon tarihi a yammacin birnin.

Hakan nan kuma rahoton ya ce gwamnatin yahudawan ta dauki wannan mataki da nufin yin wata sabuwar tsokana ga musulmi, domin kuwa daukar wannan mataki ba abu ne da mabiya addinin muslunci za su amince da shi ba, musamman ma ganin cewa wannan makabarta na da tsohon tarihi a wurin

Gwamnatin yahudawan tana yin amfani da irin goyon bayan da take samu daga manyan kasashen duniya wajen cutar al’ummar palastinu tare da danne hakkokinsu a dukkanin bangarori, ba tare da an iya gurfanar da ita a gaban shari’ar domin kwatar musu hakkokinsu ba.

Sheikh Muhammad Hussain tare da babbar cibiyar kare hakkokin palastinawa ta sanar da cewa za su dauki dukkanin matakan da suka dace domin fuskantar wannan mataki na zalunci da danniya.

Kamar yadda suka jaddad cewa daga cikin hanyoyin da za su bi da kuma matakin da za su dauka kuwa har da na sharia, wannan cibiyar ta ce a tarihin yankin baki babbu wani wanda ke ja ko musun cewa wannan makabarta ba ta mabiya addinin muslunci ba ce.

3328318

Abubuwan Da Ya Shafa: Qods
captcha