IQNA

Wasu Matasa Biyu Kiristoci Sun karbi Addinin Musulunci A Kasar Morocco

23:55 - July 17, 2015
Lambar Labari: 3329005
Bangaren kasa da kasa, wasu matasa biyu mabiya addinin kirista daya dan kasar faransa dayan kuma dan kasar Switzerland sun karbi addinin muslunci a kasar Morocco.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Morocco News cewa, wadannan matasa biyu sun karbi addinin muslunci ne a babban masallacin Katibah da ke kasar a bainar dubban jama’a, inda suka karanta Kalmar shahada biyu.

Dan kasar faransa ya zabi sunan Adam a matsayin sunan da yake son a sanya masa bayan musuluntarsa, yayin da shi kuma matashin Switzerland dan shekaru 23 mai suna John ya zabi sunan Mustafa a matsayin sunansa na muslunci.

Bisa ga wannan rahoto a kowace shekara ana samun mutane da suke zuwa daga nahiyar turai suna karbar addinin muslunci a wanann masallaci na Katibah da ke kasar Morocco, wanda hakan ta fi kasancewa a cikin watan azumi.

A cikin shekarun baya-bayan ann da dama daga cikin mutanen da ba musulmi sukan yi tafiya zuwa wannan yankin domin kara samun masaniya dangane da addinin muslunci, daga karshe kuma sai su muslunta.

3328629

Abubuwan Da Ya Shafa: Moroco
captcha