IQNA

Charlie Hebdu: Ba Za Mu kara Watsa Hotunan Batunci Ga Musulunci Ba

23:42 - July 19, 2015
Lambar Labari: 3330193
Bangaren kasa da kasa, Laurent Sorisso baban editan jaridar Charlie Hebdu ta kasar Faransa ya ce daga yanzu ba za su kara watsa hotunan cin zarafi ga addinin muslunci ba.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Shafaqna cewa, Sorisso a tattaunawarsa da jaridar Washington Post ya bayyana cewa manufarsu ba cin zarafin addinin muslunci b ace, abin da suke yi yana da alaka da yancin bayyana ra’ayi domin nishadantar da jama’a amma daga yanzu ba za su kara yin hakan ba.

Kafin wannan loacin Ronald Lozir daya daga cikin masu zanen batunci na wannan jarida ya bayyana ba zai kara yin wannan aiki da ke bakantawa musulmi rai, domin kuwa abin da suke yi suna yinsa domin nishadi, tun da ya zama da bacin ran ya bari.

Idan ba a manta a kwanakin baya wasu sun kai hari kan babban ofishin jaridar da ke kasar faransa inda suka kashe mutane 12 har lahira, da nufin daukar fansa kana bin da suke na batunci ga manzon Allah.

Wadanda suka kaddamar da hare-haren dai sun kashe bababn editan jaridar a lokacin tare da wasu ma;aikata da kuma wani jami’in yan sanda da ke gudanar da aikin tsaro a wurin, kafin daga bisani su ma a kashe su bayan yin musayar wuta.

Abin da ya faru dai ya zama babban abin da tashin hankali a burnin, amma kuma duk da hakan wannanba zai taba zama dalili na ci gaba da cin zarafin manzon Allah da suna yancin fadar albarkacin baki ba.

3330156

Abubuwan Da Ya Shafa: faransa
captcha