IQNA

An Fara Gudanar da wani Shiri na Bayar Horon Kur’ani A Jordan

23:38 - July 20, 2015
Lambar Labari: 3331510
Bangaren kasa da kasa, an fara gdanar da wani shiri na horar da dalibai karatun kur’ani mai tsarki da ilmominsa da kuma ilmin hadisi da tafsirin kr’ani mai tsarki a masallatan birnin Amman na Jordan.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafion sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran gwamnatin Jordan cewa, a jiya ne aka fara gdanar da wani shiri na horar da dalibai karatun kur’ani mai tsarki da ilmominsa da kuma ilmin hadisi da tafsirin kr’ani mai tsarki da fikihu da tarihin manzo da kuma kaidojin harshen larabaci.

Ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar da kuma babban cibiyar kula da harkokin koyarwa da bayar da horon ilmomin addini ne suka dauki nayin shirya wannan horo, wanda dalibai daga sassa na kasar a kuma matsayin karatu daban-daban suke samun horon.

Sheikh Yahya Al-kadhi daya daga cikin manyan jami’a ia  ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ya bayyana cewa, baya ga horo kan karatun kur’ani akwai horo kan al’adu, tarbiya, kimiyya da sauransu da ake koyar da daliban.

3330298

Abubuwan Da Ya Shafa: jordan
captcha