IQNA

Sahyuniyawa Na Shirin Gina Wani Wurin Shakatawa A Kusa Da Masallacin Quds

23:40 - July 20, 2015
Lambar Labari: 3331511
Bangaren kasa da kasa, yahudawan sahyuniya na shirin gina wani wurin shakatawa a yankin Salwan da ke kusa da masallacin quds mai alfarma lamarin da ya sanya palastinawa cikin damuwa.


Kamfanin dillancin labaran iqn aya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sky News Arabic cewa, yanzu haka sahyuniya na shirin gina wani wurin shakatawa mai fadin kilo mita dubu 15 a kusa da masallacin quds mai alfarma.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan wuri zai kunshi wasu daga cikin wuraren tarihi da ska hada fadojin halifofin Bani Umayyah da kuma wasu muhimman wuraren tarihi na Quds da ke yankin, wanda za s gina a cikin yankin salwan.

Najeh Bukairat babban darakta na ma’aikatar da ke kula da harkokin birnin Quds ya bayyana cewa, wannan yanki bas hi da wata alaka da yahudawa, kamar yadda fadojin halifofin bani Umayyah ba su da wata dangantaka da yahudawan sahyuniya.

Mutanen birnin Quds suna cikin damuwa, musamman ma ganin cewa aiwatar da wannan shiri zai kai ga rushe gidajen palastimawa da dama da ke yankin.

3330380

Abubuwan Da Ya Shafa: Qods
captcha