IQNA

Daesh Haihuwar Alkaida Taliban da kuma Nusra / Saudiyyah Tushen Takfiriyyah

23:47 - July 22, 2015
Lambar Labari: 3332261
Bangaren kasa da kasa, mataimakin shugaban kasar Iraki ya bayyana kungiyar yan ta’adda ta daesh da cewa an haifar da ita ne ta hanyar kungiyoyin yan ta’adda da suka gabace ta.


Kamfanin dilalncin labaran ian aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Awa cewa, Nuri Maliki mataimakin shugaban kasar Iraki ya bayyana kungiyar yan ta’adda ta daesh da cewa kngiyoyin ‘yan ta’adda ne suka samar da ita.

Ya bayyana hakan en a lokacin da yake gabatr da wani jawabi a kasar Iraki, inda y ace idan aka dubi ayyukan da wannan kungiya take aiwatarwa, za a ga cewa ba su da banbanci da na kngiyoyin yan ta’adda da aka sani kafinta, irin su Alkaida Taliban da kuma Nusra.

Wadda ita ma akidunta da ayyukanta irin na su ne baki daya, ya ce dukkanin wadanda kungiyoyi na ta'addanci sna aiwatar da manfofin wasu kasashe ne da ke nufin rusa al'ummar musulmi baki daya, kuma abin ban takaici ne shi ne wasu daga cikin kasashen larabawa musamman ma Saudiyya ne suke daukar nauyinsu.

Dangane da batun mayakan sa kai kuwa da suke taimaka ma sojojin kasar Iraki Maliki ya bayyana cewa, idan har aka rusa su to hakan yana nufin rusa kasar Iraki, domin kwa dukkanin nasarorin da sojoji ke samu, yana da alaka da taimakon sojojin sa kai.

Wannan furuci ya zo sakamakon abubuwan da wasu ke fada na neman a rusa su saboda abin da suke cewa dukaknin sojojin sa kan yan shia ne.

3332088

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki
captcha