IQNA

Taron kasa Da Kasa Domin Fada Da Tsatsauran Ra’ayi A Algeria

23:52 - July 22, 2015
Lambar Labari: 3332265
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taro a kasar Algeria dangane da tsatsauran ra’ayi da kuma hanyoyin da za a bi domin magance a shi a cikin kasashen duniya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alnahar cewa, nan ba da jimawa ba za a gudanar da wani zaman taro a kasar Algeria tare da halartar mutane daga kasashe kimanin 50 dangane da tsatsauran ra’ayi da kuma hanyoyin da za a bi domin shiga kafar wando da hakan.

 

Taron dais hi ne irinsa na farko da za a gudanar a wannan kasa a mataki na duniya wanda zai samu halartar masana domin samo bakin zaren tunkarar matasalar da ake fuskanta a halin yanzu a cikin kasashen msuulmi da sauran kasashen duniya baki daya na ta’addanci da sunan addini, sakamakon tsatsauran ra’ayi.

Wannan ya zo bayan la’akari da masana suka yi kan cewa magance wannan matsala na bukatr yin amfani da hanyoyi na ilimi da wayar da kai da kuma fadarkarwa, domin kuwa abu wanda yake da alaka da irin mummunar akida da ake cusa ma mutane da sunan addinin muslunci.

 

Ko shakka babu babu yin amfani da karfi a kowane lokaci ko kuma yin amfani da shi kadfai domin kawo karshen wannan matsala ba zai amfanar ba, mai yiwuwa ma hakan ya kara tsanantar matasalar a duniya musamman ma a cikin kasashen musulmi.
Bayan sanar da cewa za a gudanar da wannan taro, yanzu haka dai an aike da goron gayyata gam asana da malamai daga kasashe daban-daban domin halartar taron, tare da gabatar da kasidu da za su taimaka wajen ilmantarwa da kuma wayar da kan matasa musamman, wadanda su ne ake ruwar da sauri.

3331814

Abubuwan Da Ya Shafa: aljeria
captcha