Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Manama Post cewa, a cikin wani bayani da suka fitar , gugun matasan 14 ga watan Fabrairu sun mayar wa mahukuntan kasar da martini kan cewa Sudiyya ce ke da alhakin rusa masallatai da kuma kara ruruta wutar rikici a kasar ba Iran ba kamar yadda mahukunta na Bahrain suke rayawa.
Bayanin nasu ya ci gaba da cewa, babu wani dalili da zai sanya mahukuntan Bahrain su zargi Iran da haifar da wata matsala a cikin kasar, domin kuwa tun farko mahukuntan kasar sun gayyaci Saudiyya domin ta zo ta ci zarafin al’ummar wannan kasa da lasisi tare da keta alfarmar wurare masu tsarki.
Matasan ska ce a kowane lokaci Iran tana fadar gaskiya kuma tana tare da dukkanin al’ummomin da ake zalunta a koina suke, wanda hakan ke tabbatar da cewa mahukntan kasar Bahrain sun rasa makama, sakamakon abin da ska jawo ma kansu na fushin al’ummar kasar.
Tun bayan fara boren neman sauyi a kasar ta Bahrain, mahukuntan kasar sun gayyaci wasu daga cikin kasashen larabwa da su taimaka musu wajen murkushe masu neman sauyi na adalci a bangaren siyasa akasar, kuma Saudiyyah ce ta shiga a gaba domin aiwatar da hakan, inda aka kame tare d akashe dubban mutane kasar da suke neman hakkokinsu.
Gungun matasan 14 ga Fabrairu ya jadda cewa babu gudu babu ja da baya dangane da neman sauyi ta hanyar lumana, har sai al’ummar kasar Bahrain ta samu yancinta da kuma dukkanin hakkokinta da aka tauye, kuma ba za su taba bari a tsokane su kamar yadda mahukuntan ke kokarin yi.
3335622