IQNA

Jami’ar Cambriege Ta Birtanita Za Ta Shirya Tattaunawar Addinai

23:57 - August 02, 2015
Lambar Labari: 3338096
Bangaren kasa da kasa, jami’ar Cambriege a kasar Birtaniya za ta shiryawa wani zama kan tattaunawa tsakanin addinai da nufin samar da fahimtar juna.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Daily Times cewa, masana a jami’ar Cambriege a kasar Birtaniya za su shiryawa wani zama kan tattaunawa tsakanin addinai da nufin samar da fahimtar juna a tsakaninsu.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na daga cikin irin kokarin da masana da masu bincike kan harkokin addinai da al’adun al’ummomi a jami’ar suke yi da nufin kara kusanto da fahimtar juna tsakanin sauran addinai na duniya da juna wanda za a yi a 2015 kamar yadda aka saba.

Da dama daga cikin al’ummomi sun gamsuwarsu da wannans hiri tare da bayayna shi da cewa yana da matukar muhimamnci idan aka yi laka’ari da yadda zai taiamka wajen kara kusanto da ahimta tsakanin al’ummomi.

Kuma samun wannan damar za ta sanya kowa ya bayyana mahangarsa kana bubuwa da dama suke wakana, musamman ma musulmi wadanda ake takura musu a wasu kasashe na turai, sakamakon abin da wasu suke yi na ayyukan ta’addanci da sunan addinausu.

Daga cikin wadanda za su halartahar da kungiyoyin mabiya addinin muslunci da kuma yahuwada gami da kiristoci da dai sauransu, wanda hakan yake da matukar muhimanc. Hakan daga kasashen Oman, Indonesia, Yemen,Nigeria, Pakistan Palastine, Singapore, Swede, England da dai sauransu.

3337526

Abubuwan Da Ya Shafa: UK
captcha