Kamfanin dilalncin labaran iqn aya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Saba Net cewa, Sayyid Abdulmalik Alhuthi y ace Isr’ila ita ce mai amfana kai tsaye da hare-haren da mahukuntan saudiyyah suke kaddamarwa kan al’ummar kasar, kuma daga karshen al’umma ce za ta samu rinjaye kan mas shishigi da yardar bangiji.
Jagoran na Ansarullah ya ce makiya mutanen yemen ne a karshe zasu yi asara a yakin da kasar saudia da kawayenta suka dorawa mutanen kasar.
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ne ya bayyana haka a jiya Lahadi a wani jawabin da ya yiwa mutanen kasar ta tashar television na kungiyar.
Al-hutha ya kara da cewa mutanen kasar Yemen ne zasu sami nasara daga karshen don sun shiga wannan yakin ne don nemawwa kansu da kasarsu encin kai. Zasu sami nasara ne don su aka zalunta.
Danagne da abinda yake faruwa a birnin Aden wanda wasu sassansa da csuke karkashen ikon saudia da magoya bayanta kuma, Abdulmalik Al-Huthi ya ce, nasarar da saudia da samua a wani bangare da birnin Aden na wucin gadi ne da sannan zasu rasa wannan nasarar.
Mutane akalla 4000 ne suka rasa rayukansu ya zuwa yanzu mafi yawansu mata da yara a hare haren na kasar saudia take kaiwa kan Yemen tun ranar 26-Maris da ya gabata.
Sayyid Abdulmalik Alhuthi y ace a shirye su karbi duk wani bangare da ya gabatr da shawara domin samun matsaya ta siyasa domin warware rikicin kasar ko da daga wajen kasashen larabawa ne, domin kuwa larabawa sun kasa.
A lokacin da yake yin kira ga mutanen kudancin kasar kuwa, ya bayyana musu cewa da su san abin da Saudiyyah yi yaudara ce kada su fada acikin tarkonta, domin tana son ta yi amfani da su domin rusa kasarsu.