Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Independent cewa, Galawi fitaccen dan siyasa akasar Birtaniya ya yi kakkausar suka dsangane da kisan jariri da yahudawa suka yi Palastinu tare da bayyana hakan da cewa yana a fili jinin palastinawa yana da arha.
A nasa bangaren kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya tare da amincewar dukkanin mambobinsa sha biyar da suka nuna bacin ransu, bai yi wata-wata ba wajen yin tir da Allawadai da wannan danyen aiki na yahudawan sahyuniya.
Kamar yadda sakatare janar na Majalisar dinkin duniya a cikin fushi ya yi Allawadai da hakan, inda ya ce siyasar gwamnatin Isra’ila ta mamaye yankunan palastinawa ita ce kara karfafa gwiwar yahudawa masu tsatsauran ra’ayi aikata irin wannan ta’asa.
Ita kuniyar tarayyar turai da kuma kungiyar hadin kan kasashen larabawa da kungiyar kasashen musulmi, duk suka fitar da bayanai da ke yin tir da Allawadai da kakkausar murya kan hakan, tare da dora alhakin abin da ke faruwa na cin zarafi a kan fararen hula palastinawa a kan salon siyasar gwamnatin yahudawa.etanyahu.
Fushi da bacin rai mai tsanani kan kisan Ali Sa’ad Dawabisha dan watanni 18 da haihuwa da kone dan uawansa dan shekaru 4 na bayyana daga al’ummomin duniya da suka hada har da sauran kasashen yammacin turai da ke bai wa Isra’ila kariya ido rufe suka nuna kan wannan aiki na ta’addancin yahudawan sahyuniya na kisan jariri bapalastine ta hanyar kone shi da wuta.
3338227