IQNA

Ta’addanci Barazana Ce Ga Dukkanin Iyakokin Kasashen Afirka

23:36 - August 10, 2015
Lambar Labari: 3341150
Bangaren kasa da kasa, Nuzha Al-alawi ya bayyana cewa matsalar tsatsauran ra’ayi tana yin barazana ne ga dukkanin iyakoki na kasashen Afirka baki daya.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa Nuzha Al-alawi jakadan kasar Morocco a kasar Ghana ya bayyana cewa matsalar tsatsauran ra’ayi tana yin barazana ne ga dukkanin iyakoki na kasashen nahiyar Afirka baki daya ba tare da banbanci ba.

Ya ci gaba da aiki ne da ya rataya kan dukkanin kasashen nahiyar Afirka baki daya, kamadaga gabaci arewaci da kudanci da kuma yammacin nahiyar su shiga kafar wando daya da duk wani aiki na tsatsauran ra’ayi da ke kai matasa zuwa ga ta’addanci.

Jakadan an Morocco a kasar Ghana ya ce kasarsa tana yin dukaknin kokarinta domin tabbatar da cewa ta safke nauyin da ya rataya  akanta wajen kara kusanto da kasashen anhiyar da kuma wayar da kansu kan muhimman lamurra da suka shafe su baki.

Ya ce za su ci gaba da yin hakan domin tabbatar da cewa an samu zaman lafiya mai dorewa a cikin dukaknin kasashen Afirka baki daya, haka nan kuma za su ci gaba da yin ayyuka na ilamatrwa daidai da koyarwar addinin domin kowa ya gane cewa ta’addanci bas hi da addini.

3340868

Abubuwan Da Ya Shafa: ghana
captcha