IQNA

Al Saud Ba Su Iya Durkusar Da Iran Ba Duk Da Kudaden Da Suke Kashewa Kan Hakan

23:37 - August 10, 2015
Lambar Labari: 3341151
Bangaren kasa da kasa, Rasem Nafis daya daga cikin masana a kasar Masar ya bayayna cewa duk da irin makudan kudaden da gwamnatin masarautar Al Saud ke kashwa da nufin gurgunta Iran hakan bai yi nasara ba.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na aynar gizo na Safakuna cewa, Rasem Nafis wani masani dan kasar masar kuma mabiyin mazhabar shi’a ya bayyana cewa, duk da irin makudan kudaden da gwamnatin masarautar Al Saud ke kashwa da nufin gurgunta Iran hakan bai yi nasara ba kuma ba za ta yi ba.

Masanin ya ci gaba da cewa, mahukuntan Saudiyya bas u da fahimta, domin kuwa tsawon shekaru suna ta rura wutar rikici da yaki a yankin gabas ta tsakiya domin cimma manufofinsu, amma har yanzu ba su yi nasara ba, illa asara da suke ta yi.

Daya daga cikin manyan kurakuran da suka tafka shi ne yadda suka taimaka ma Saddam Hussainya yi yaki da kasar Iran har tsawon shekaru takwas, kuma shi da su duka suka sha kashi, kamar yadda suka kunna wutar rikici a kasar Syria da nufin rusa wanann kasa, amma bayan wucewar shekaru biyar har yanzu ba su nasara ba, haka nan kuma a yemen ba za su nasara ba.

Rasem Nafis ya ce masarautan Al saud bas u san awani abu ba in banda yaki da kisa da rusa yankin baki daya, amma kuma da sannu za su gane kuransu kamar yadda suka far gani a halin yanzu, domin kuwa dukkanin abin da suka kulla zai dawo kansu abbu makawa.

3340895

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha