IQNA

Wani Dan Kasar Spain Da Yaransa Biyu Sun Karbi Muslunci A Kasar Morocco

23:41 - August 10, 2015
Lambar Labari: 3341153
Bangaren kasa da kasa, Wani bature dan kasar Spain tare da 'ya'yansa biyu sun tafi kasar Morocco domin yawon shakatawa inda suka karbi addinin musulunci.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo na Marakesh World News cewa, Wani bature dan kasar Spain tare da 'ya'yansa biyu mace da namiji, sun shelanta karbar addinin musulunci a wani masallaci a birnin Aljadida mai tazarar kilo mita 90 daga birnin kazablanka na kasar Morocco.

Wanann lamari dai ya faru ne a ranar juma inda suka yi sallar zuhur a garin a wannanmasalaci da suka musluncta, inda aka yi ta yada hotunansu a cikin shafin Youtube, kuma sun hakan ya bar bababn tasiri a cikin zukatan mutanen da ke wurin baki daya, sun kuma canja sunayensu zuwa sunayen musulunci.

A cikin yan lokutan nan dai ana samun mutane suna karbar addinin muslunci a cikin kasar ta Morocco da suke zuwa yawon shakatawa a kowane lokaci a birane daban-daban na kasar, sakamakon irin yadda suke ganin muslulmi da al’adunsu da dabiunsu irin na muslunci.

A cikin bazarar da ta gabata wasu mutane biyu yan kasar faransa da Switzerland sun zo kasar inda suka karbi addinin muslunci a masallaci Kutaibah na kasar ta Morocco.

3341034

Abubuwan Da Ya Shafa: Moroco
captcha