IQNA

Ma’aikatar Ayyukan Addini Ta Palastinu Ta Yi Allawadai Da Rufe Masallacin Annabi Ibrahim

19:34 - August 11, 2015
Lambar Labari: 3341288
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Yusuf Adis ministan mai kula da ayyukan addinin muslunci na palastinu ya yi Allawadai da kakkausar murya dagane da shirin yahudawan sahyuniya na hana musulmi shiga masallacin Annabi Ibrahim.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, gwamnatin yahudawan sahyuniya na shirin rufe masallacin annabi Ibrahim daga karfe 22 na Laraba zuwa 22 na ranar Alhamis, tare da hana musulmi gudanar da ayyukansu na ibada  aciki, bisa hujjar cewa a lokacin yahudawa za su gudanar da tarukansu na idin yahudawa a cikinsa.

Sheikh Yusuf Adis ya ce babu tantama kan cewa masallacin annabi Ibrahim na al’ummar musulmi ne, kuma duk wani abin da yahudawa za su yi ba zai sanya wannan wuri mai tsarki ya zam mallakinsu ba, kuma yana kira ga dukkanin musulmi da su dauki matakan da suka dace domin takawa yahudawan birki.

Ya ci gaba da cewa wannan bas hi ne karon farko da yahudawan sahyuniya suke yin irin wannan ta’asa ba, sun saba yin hakan ta yadda har ma suka hana yin kiran salla a wasu lokutan, kamar yadda kuma sukan kai ma muslmi masallata hari a wasu lokutan.

Ministan na palastinawa ya ce manufar wannan yunkuri na yahudawa ita ce hankoronsu na mayar da wannan wuri mai tsarki wata majami’a ta yahuadawan sahyuniya, wanda kuma hakan lamari ne da musulmi ba za su taba  amincewa da shi ba.

Sheikh Yusuf Adis ya ce yana yin kira da kakkausar murya ga kasashen muslmi da su dauki matakin matsa lamba kan yahudawan sahyuniya kan wannan lamari, tare da hana su ci gaba da keta alfarmar wanna wuri da sauran wurare masu tsarki.

3341090

Abubuwan Da Ya Shafa: palestine
captcha