IQNA

Kaiwa Masallatai Hari Ya Nuna Cewa ‘yan Ta’adda Da Musulunci Suke Kiyayya

23:52 - August 12, 2015
Lambar Labari: 3341754
Bangaren kasa da kasa, a cikin wani bayani da malaman mazhabar shi’a na yakin Qatif a gabacin Saudiyya ska fiyar sun bayyana cewa kai haria masallacin Abaha ya taabtar da cewa yan ta’adda da musulunci suke fada.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na labarin Qatif cewa, malaman addinin muslunci na mazhabar shi’a da Sunnah sun fitar da bayani kan da ke yin Allawadai da harin ta’addancin da aka kai garin Abha a gundumar Asis a makon da ya gabata.
Kimanin malamai 43 na Sunnah da shi’a ne suka fitar da bayani na yin tir da wannan aiki na ta’addanci wanda ya yi sanadiyyar j ami’an tsaro na kasar Saudiyya ne suka rasa rayukansu a yau a lokacin da wani mutum da ya yi jigidar bama-bamai ya tarwatsa kansa a cikin wani masallaci na jami'an tsaron kasar.

Majiyoyin ma’aikatar harkokin cikin gida a kasar ta Saudiyyah sun ce mutumin ne ya tayar da bama-baman da ke jikinsa a cikin masallacin a garin Abha da ke cikin gundumar Asir a kudancin kasar.

 

Kungiyar ‘yan ta’addan IS ta fitar da sanarwar cewa ita ce ke da alhakin kaddamar da harin, kuma ta sha alwashin ci gaba da kai hare-hare a cikin kasar ta Saudiyya, inda a halin yanzu suke kafirta hatta da mahukuntan na Saudiyyah.

Tun kafin wannan lokacin dai gwamnatin Saudiyyah ta nuna damuwa matuka dangane da abin da ka iya zuwa ya dawo sakamakon shiga cikin kungiyoyin ta’addanci matasan kasar ke yi, inda su ne suka fi a yawa  a tsakanin ‘yan ta’adda da ke kai hare-haren yankin wanda kuma wasu daga cikinsu suna komawa gida, bayan samun gogewa kan ayyukan ta’addanci.

 

3341359

Abubuwan Da Ya Shafa: qatif
captcha