Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palestine On line cewa, Hana Isa malamin dokokin kasa da kasa kuma babban sakaren kwamitin kare Quds da wurare masu tsarki na mslmi da kirista, ya bayyana Isra’ila a matsayin sanadin duk wani tashin hankali a yankin baki daya.
Y ace hankoron Isra’ila na mayar da masallacin quds da sauran wurare masu tsarki mallaki musulmi da kuma mabiya addinin kirista, shi ne bababn abin da ya jawo dukkanin matsalolin da ake fama da su, wanda kuma bai kamata a yi shiru kan lamarin ba.
Han Isa ya ce ministan yakin haramtacciyar kasar Isra’ila Moshe Yaalon ya bayyana cewa, masallacin annabi Ibrahim mallakin yahudawa ne, bayan hakan ne wasu daga cikin yahudawa suka kai farmaki kan mabiya addinai na muslnci da kiristanci ayankin suka ci zarafinsu.
Wannan ya nuna cewa abin da yake faruwa na cin zarafin muslmi da kiristoci a cikin yankunan palastinawa ba batun aikin yahudawa masu tsatsauran ra’ayi ba ne, hakan siyasa ce ta Isra’ila, domin kuwa gas hi ministan yaki da kansa ya frta haka, wanda ke nuni da cewa mahanrsyu Kenan.
Ya ci gaba da cewa Isra’ila mafarkinta ya kusa tababta, na mayar da asallcin annabi Ibrahim majami’ar yahudawa, tare da gina wani wurin bauta na karya a masallacin quds mai alfarma.
3341697