Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ma’an cewa, kotun haramtacciyar kasar Isra’ila ta haramta wa wasu matasa palastinawa mace guda da kuma matasa maza biyu zuwa massalcin Aqsa mai alfarm da tazzarar kwanaki tsakanin 45 zuwa 60, kamar yadda ta haramta wani bapalastinan shiga masallacin na tsawon watanni 6 a jere.
Ramzi Ktailat daga kungiyar farar hula ta Qudsuna ya bayyana cewa Saiham Audah kotun haramtacciyar kasar Isra’a ta fitar da hukunci a kanta aranar talata da ta gabata na hana ta zuwa masallacin har tsawon watanni biyu a nan gaba.
Haka nan kuma kotuna ta haramta wa wasu matasa Musatafa Sayyad dan shekaru 18 da kuma Adsam Hamdi Abu Ramila dan shekaru 15 zuwa masallacin har tsawon kwanaki 45 a jere, da hakan ya hada da cikin masallacin da kuma harabarsa.
Bayan nan kuma wani bapalastinen shi ma mai sna Tamer Shalata bayan kame shi tare da mika agaban kotun , ta yanke masa hkuncin shiga masallacin quds har tsawon watanni 6 a nan gaba, kamar yadda aka yanke wa sauran, tare da hana shi kusantar masallacin baki daya a cikin wadannan watanni.
3341821