IQNA

Mamban Fatawa A Haram: Shagaltuwa Da Ayyukan Tunawa Da Magabata A Hajji Shirka Ne

20:12 - August 14, 2015
Lambar Labari: 3342981
Bangaren kasa da kasa, Muhamamd Almas’udi daya daga cikin ammbobin kwamitin da ke bayar da fatawa a haramin Makka mai alfarma ya ce yin duk wani aiki na tunawa da magaba a cikin aikin haji shirka ne.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Shafaqna cewa, Muhammad Mas’udi malamin fikihu da usul kuma mamba a kwamitin da ke bayar da fatawa a haramin Makka mai alfarma ya ce yin duk wani aiki na tunawa da magaba a cikin aikin haji kamar daukar hotuna da sauran aiki ne na riya, kuma hakan shirka ne a cikin bautar Allah.

Ya ce wadanda suke daukar hotuna a lokacin aikin haji hakika wadannan suna yin aikin riya ne, kuma aikin riya  acikin ibada yana rusa wannan aiki, saboda ahaka  cewarsa yin hakan shi ne zai kai aikinsu zuwa ga rushewa.

Ya kara da cewa a lokacin da ake gudanar da aikin haji da sauran ayyukan ziyara a wanann wuri, dole ne ya zama zuciyar mai aikin tana wajen ubangiji ne baki daya, kuma yin duk wani an riya to karamar shirka ce.

Wannan bai shi ne karon farko da malaman fadar masarautar kasar da ake kira malaman harami suke bayar da irin wadannan fatawowi masu ban mamaki ba, domin kuwa hatta da sauran ayyukan da addinin ya tabbatar sukan haramta su bisa son ransu.

3342919

Abubuwan Da Ya Shafa: makka
captcha