IQNA

An Fara Taron Kasa Da Kasa Domin Hana Fatawowin Da Ke Haifar Da Ta’addanci A Masar

20:00 - August 18, 2015
Lambar Labari: 3345835
Bangaren kasa da kasa, an fara gudana r da wani bababn taro na kasa da kasa da malamai ke gabar da bayanai kan yadda za a bullowa masu bayar da fatawowyi na tsattsauran ra’ayi a Masar.


Kamfanin dillancin labaran iqa ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na PressTV cewa, an fatra gudana r da babban taron kara wa juna sani kan shiga kafar wando daya da fatawowyin da ke karfafa yan ta’adda.

Ibrahim Najm babban mai bayar da shawara ga mai bayar da fatawa na Masar y ace, shi dai wannan taro an fara gudanar da shi ne a mataki na duniya tare da halartar malamai da ke gabar da bayanai kan yadda za a bullo wa masu bayar da fatawowyi na tsattsauran ra’ayi dfa ke kai ga haifar da a bin da ke gani halin yanzu.

Wannan taron kara wa juna sani yana yin dbi kan irin hadarin da wadannan fatwowi suke da shia  cikin al’ummar musulmi da kuma barnar da ska yi ya zuwa yanzu, ta hanyar karkatar da tunanin mata da dama a duniyar musulmi tare da cusa mus akidar ta’addanci da kafirta musulmi.

Malamin ay ci gaba da cewa idana ka duba a bin da yake faruwa a kasashen Iraki da Syria da Masar da kuma Libya a lokacin za a kara fahimtar mummunan tasirin tasirin irin wadannan malamai da kuma muggan fatawowin da suka baiwa matasa da suke aikata wannan ta’asa  awadannan kasashen larabawa.

Ahmafd babban malamin cibiyar Azhar a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a jiya a wrin taron ya bayyana cewa, aikin dukkanin muslmi su mike tsaye domin fada da wannan mummunar akida ta kafirta musulmi da kuma ta’addancin da masu akida suke aikatawa a cikin kasashen musulmi da ma sauran kasashen duniya.

3345663

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha