Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Lebanesetweet.com cewa, Malami da masana sun kammala wani taro dangane da fatawoyin da ake bayarwa a cikin kasashen musulmi da suke karfafa tsattsauran ra’ayi da ta’addanci, wanda aka yi a birnin Alkahira na kasar Masar a cikin kwanaki biyu.
Bayanin ya ce taron kara wa juna sani yana yin dbi kan irin hadarin da wadannan fatwowi suke da shia cikin al’ummar musulmi da kuma barnar da ska yi ya zuwa yanzu, ta hanyar karkatar da tunanin mata da dama a duniyar musulmi tare da cusa mus akidar ta’addanci da kafirta musulmi babu gaira babu sabar.
Wasu daga cikin malamai sun bayyana cewa cewa idan aka duba a bin da yake faruwa a kasashen larabawa a halin yanzu a lokacin za a kara fahimtar mummunan tasirin tasirin irin wadannan malamai da kuma muggan fatawowin da suka baiwa matasa da suke aikata wannan ta’asa awadannan kasashen larabawa musamman, fiye da kashe 50 ne suka halarci taron.
Shi ma daya daga cikin malaman cibiyar Azhar a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a jiya a wrin taron ya bayyana cewa, aikin dukkanin muslmi su mike tsaye domin fada da wannan mummunar akida ta kafirta musulmi da kuma ta’addancin da masu akida suke aikatawa a cikin kasashen musulmi da ma sauran kasashen duniya baki daya.
3347113