Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-usbu cewa, a cikin wannan makon ne aka samu bayanin cewa mai yiwuwa a daga tutar palastinu a gaban babban ginin zauren majlisar dinkin duniya a cikin watan Satumba mai zuwa kamar dai yadda majiyoyin suka tabbatar.
Wasu daga cikin wakilan wasu daga cikin kasashen larabawa da ke majalisar dinkin duniya suka gabatar da wannan bukata da nufin kara matsa lamba kan haramtacciyar kasar yahudawa da ta amince da batun kafa kasar palastinu mai cin gishin kanta.
Idan dai har wannan lamari ya tabbata, to hakan zai kara nuna wa duniya cewa a halin yanzu haramtacciyar kasar yahudawa ta zama saniyar ware, ta yadda kasashen duniya a aikace sun nuna amincewa da samuwar kasar palastinu mai zaman kanta.
Daga tutar dai bas hi nufin palastinu ta zama kasa mai cikakken iko kamar kowace kasa ta duniya, amma a siyasance hakan yana dauke da babban sako ga al’ummomin duniya, da ke tabbatar da an kama hanyar kafa kasar palastinu, kuma zaluncin da ake a kansu ya fara kawo karshe.
Bisa ga kudirin da aka gabatar ga kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, Palastinu da Vatican ne za a daga tutocinsu, a matsayin masu sanya ido a majalisar, ba a matsayin kasashe masu zaman kansu ba.
3349338