Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na On Islam cewa, bayan kwashe tsawon shekaru a na jiya a yanzu dai an kammala tare da an bude tashr talabijin ta musulmi ta farko a kasar Uganda da ke gabacin nahiyar.
Alhaji Karim Kalisa babban daraktan talabijin ta musulmi a kasar ta Uganda Salam TV ya bayyana cewa, an dauki tsawon lokaci mabiya addinin muslunci a kasar at Uganda suna jiran a gdanar da wannan aiki da aka fara tsawon shekaru, amma yanzu da yardarm ubangiji an kammala shi.
Ya ci gaba da cewa wannan aiki yana da matukar mhimmanci ga dukkanin jsulmin kasar, domin kuwa za arika watsa shiri ne wanda dukkanin mutanen kasar za su iya kallo kai tsayi daga wannan tasha, wanda kuma hakan babban ci gaba ne.
Kafin wanann lokacin y ace suna gudanar da shirye-shiryensu ta wasu kafofin yada labarai masu zsaman kansu da ake bas u mintuna ko sa’oi, musamamna cikin watan Ramadan an shekarar 2014 sun samu sa’oi shida sun ashirin muslunci.
Ya ce akwai tashoshi gda uku amma dukakninsu na yankuna ne kawai, wadanda ba za su iya gamsar da dukaknin kasar ba, saboda haka ya zama wajibi a karfafa tare da fadada ikin watsa wadannan shirin zuwa sauran yankna na kasar domin amfanin dukkanin musulmi, wanda amfara shit n sheakara ta 1993 da ta shude.
Kalisa ya kara da cewa babbar manufar bude wannan tasha ita ce yada manufofin addinin muslunci a kasar ga musulmi domin sanin hakikanin koyarwar musulmunci da kum akara ilmantar da su, ga wadanda ba musulmi ba kuma su san abin da ake kira musulunci da manufofinsa na gaskiya.
Sha’ban Usman Maniya shi ne bababn daraktan bangaren watsa labarai, ya bayyana cewa wannan tasha za ta mayar da hankali wajen bayyana hakinanin muslunci na gaskiya, sabanin abin da ake yadawa kan musulunci wand aba gaskiya ba ne.
3350831