IQNA

Musulmin Kenya Sun Jerin Gwanon Kin Amincewa Da Kisan Da Ake Yi Musulmi A Kasar

23:39 - August 30, 2015
Lambar Labari: 3354282
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci sun gudanar da gangami a gaban masallaci a ranar Juma’a a birnin nairibi fadar mulkin kasar Kenya domin nuna rashin amincewa da kisan da ake yi musu.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo na World Bulletin cewa, Amin Kimathi wani musulmin kasar Kenya mai rajin kare hakkokin mabiya addinin muslunci a kasar da shugaban majalisar musulmin kasar sun bayyana cewa, yan ta’adda su ne masu kashe babu hakki a kasar.

Ya ci gaba da cewa a kan wane dalili ne za  akashe mutumin da yake musulmi, kuma bai aikata wani laifi na kisan wani ko kyamar wani addini ko wata akida ba laifinsa kawai shi ne musulmi?

Kiamthi y ace duk wadanda suke aikata hakan sun cancan a kama su a kai su gaban kuliya domin su fuskanci hkuncin da ya dace da su daidai da kundin tsaron doka na kasa.

Y ace an gawwawakin mabiya addinin mslunci da dama  awasu yankuna na kasar wadanda ka kashe babu gaira bab sabar sai domin kawai su musulmi ne, saboda ana kallon musulmi yan ta’adda.

Y ace ba za s taba yarda da hakan ba, kuma daga yau ba za su yi shiru kan wannan batu ba har sai an dauki mataki na doka da bin kadun duk wadanda sue da hann wajen aikata wannan tabargaza tare da hukunta su.

A kasar Kenya musulmi suna fuskantar babbar matsala  acikin lokutan nan tun bayan bayyanar kungiyoyi masu tsararn ra’ayi na ‘yan ta’adda irin su kungiyar Alashab, inda wasun masu kin musulunci suke fakewa da hakan domin kashe musulmi da kuma cin zarafinsu.

3354145

Abubuwan Da Ya Shafa: kenya
captcha