IQNA

Jam’iyya Mai ra’ayin Muslunci Ta Samu Nasara A Zaben Morocco

23:47 - September 05, 2015
Lambar Labari: 3358341
Bangaren kasa da kasa, jam’iyya mai ra’ayin muslunci a kasar Morocco ta samu nasara a mafi yawan biranan kasar masu girma.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Reauters cewa, ana ci gaba da kirga kuri’u a zaben yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar a jiya, inda jam’iyya mai ra’ayin muslunci a kasar Morocco ta samu nasara a mafi yawan biranan kasar masu girma wato jam’iyyar PJD a kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa ya zuwa yanzu an kirga kimanin kasha 80 cikin dari na kuri’un, kuma a wasu yankunan kasar jam’iyyar Liberal ta samu kusan kasha 20 yayin da jam’iyyar masu kishin muslunci ta samu 17, sai a manyan birane ta fi samun kuri’a.

Masu kishin sun samu nasara manyan birane irin su Kazablanka, Tunjiz, Rebat da kuma Agadiz, wadanda ake lissafa samun nasara  acikinsu a matsayin lashe zabe a kasar.

Wannan shi karon farko da kimanin mutane dubu 32 da suka hada manyan jami’ai a kanan hukumi su 978 aka zabe su kai tsaye a kasar da ake gudanar da mulkin mulukiya.

Hukumar zabe ta kasar ta ce kimanin kasha 52 cikin na wadanda suka cancanci kada kuri’a ne suka fito a wannan zabe, wanda kuma yake kusa da wadanda suka fito a zaben shekara ta 2009.

Kasar Morocco dai ta dauki kwararn matakai tn bayan zanga-zangar da aka yi da ta kawo karshen masu mulkin kama karya  akasashen Tunisia, Libya da kuma Masar a shekarun da ska gabata, inda ta bayar da damar a gudanar da zabe domin kafa majalisar ministoci da sauran bangarori.

3358171

Abubuwan Da Ya Shafa: morocco
captcha