Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ahbarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, keta alfarmar wurare masu tsarki da Isra’ila ke yasa ya zama wajibi kan kasashen musulmi su dauki matakai na taka mata burki cikin gagawa.
A nata bangaren kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta yi Allawadai da ke alfarmar wurare masu tsarki da yahudawan sahyuniya suke yi a birnin Quds da ma sauran yankunan Palastinu, gami da cin zarafin palastinawa marassa kariya.
Babban jami’in mai kula da harkokin Palastinu a cikin kungiyar hadin kan kasashen larabawa ne ya sanar da hakan a jiya a babban ofishin kungiyar da ke birnin Alkahira na kasar Masar, inda ya ce kungiyar tana nuna takaicinta matuka dangane da yadda yahudawan sahyuniya suke ta tsananta ayyuknsu na cin zarafin Palastinawa da yi musu kisan gilla, da kuma keta alfarmar wurare masu tsarki.
Ya ce kungiyar za ta ci gaba da bin dukkanin hanyoyi da suka dace domin kalubalantar gwamnatin yahudawan Isra’ila da nufin taka mata birki kan wannan ta’asa.
A nata bangaren kungiyar kasashen musulmi ta ce za ta gudanar da wani zama nan ba da jimawa ba akasar magarib domin yin dubi kan abubuwan da suke faruwa a palastinu, musamamn a birnin mai alfarma.
3358420