IQNA

Musulmin Malawi Za Su Fara Wayar Kan Mutane Kan Batuncin Da Ake Yi Musu A Kafofin Sadarwa

21:50 - September 07, 2015
Lambar Labari: 3360210
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci na shirin fara aiwatar da wani shiri na wayar da mutanen kasar dangane yadda suke fuskantar matsaloli sakamakon bata sunansu a kafofin sadarwa.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam cewa, Sheikh Jufliyyah Kuwawangir babban daraktan cibiyar  kula da yada harkokin addinin muslunci a kasar Malawi cewa musulmi na shirin fara aiwatar da wani shiri na wayar da mutanen kasar baki kan yadda suke fuskantar matsaloli sakamakon bata sunansu da watsa bayanai na karya a kansu a kafofin yada labarai na kasar.

Ya ci gaba da cewa tun kafin wannan lokacin musulmi suna fuskantar matsaloli wadanda ba a rasa ba, amma a halin yanzu duk abin da musulmi za su shiga a cikin kasar su ne koma baya, a kan haka za su bullo da sabbin hanyoyi na wayar da kan jama’a kan muslunci.

Daga cikin hanyoyin da za su bi kowa har da amfani da kafofin sadsarwa na zamani da suka hada yanar gizo da kuma tarukan manema labarai, domin bayyana hakikanin fuska ta addinin muslunci da kuma koyarwarsa, maimakon abin da ake yadawa kan muslunci maras tushe.

Wasu daga cikin kafofin watsa labarai na kasar na gwamnati da kuma masu zaman kansu, suna yada labarai na karya dangane da musulmi domin kawai su cimma wasu manufofi na bata sunan muslunci a idon sauran al’ummomin kasar, wanda kuma hakan yana yin mummunan tasiri ga musulmin.

Musulmin kasar Malwi dais u ne kasha 36 cikin dari na dukkanin al’ummar kasar da yawansu kai miliyan 15 a halin yanzu.

3358855

Abubuwan Da Ya Shafa: malawi
captcha