IQNA

22:20 - September 11, 2015
Lambar Labari: 3361263
Bangaren kasa da kasa, majaliasar dinkin duniya ta amince da daftarin kdirin da wasu kasashen larabawa suka gabatar duk kuwa da rashin amincewa Isra’ila da Amurka kan daga tutar Palastinu.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sky News Arabic cewa, a jiya majalisar dinkin duniya ta kada kuri’a inda kasashe 119 suka amince 45 kuma suka yin gum da bakinsu 8 kuma suka ki amincewa da daga tutar palastinu a gaban zaurn majlaisar.

Wanann lamari ya zama wata babbar nasara ga al’ummar palastinu da ma sauran al’ummomin duniya masu adawa da zalunci da mulkin mallaka na kasashen yammacin turai da suka kafa wannan haramtacciyar kasa kuma suke mara mata baya.

Kasashen da suka ki amincewa da wannan daftarin kudiri kuwa sun nuna wa duniya a bayyane cewa su ne suke da hannua  dukkanin ayyukan ta’addancin da wannan haramtacciyar kasa take aikatawa kan raunana, yayin da kuma wasunsu rashin ‘yancin siyasa ne.

Tun bayan sanar da hakan , dbban palastinu a cikin yankunasu da ma sansanoninsu a cikin kasashe makwafta suna ta murna da hakan, tare da fatan ganin an samu babbar nasara ta kawo karshen mulkin zalunci da danniya  akansu na yahdawa sahyuniya.

Fiye da shekaru sattin ne da al’mmar palastinu suke karkashin mamaya ta yahhudawa da ke samun goyon baya da taimako daga manyan kasashe nay an mulkin mallaka.

3361186

Abubuwan Da Ya Shafa: UN
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: