Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Akhbar Yemen cewa, ma’aikatar kula da ayyukan addini ta Yemen ta sanar da cewa, wadanda aka hana zuwa hajji daga kasar a wannan shekara sun bayar da kudin domin Karin taimako ga rundnar sojin kasar domin mayar da martini kan Saudiyya.
Mahkuntan an Saudiyya sun dauki wannan mataki ne domin hana yan kngiyar Ansarullah zuwa hajjin bana su kimanin dubu 160, saboda tsoron da suke ji na kada a mayar da martini a kansu kan kisan kiyashinda suke kan mata da kanan yara acikin kasar ta Yemen a halin yanzu, wanda kasashen duniya baki da suka yi gum da bakunansu sai kadan daga cikin masu yancin siyasa.
Majiyar asibitin Yeman ta yi gargadi kan karin tabarbarewar harkar kiwon lafiya a lardin taiz da ke kudu maso yammacin kasar saboda karancin kayayyakin aiki da magunguna tare da rufe wasu asibitoci bakwai a sassar lardin sakamakon hare-haren wuce gona da iri da jiragen saman yakin kasar Saudiyya ke ci gaba da kai wa kan yankuna daban daban na kasar.
Majiyar asibitin lardin na taiz ta kara da cewar a halin yanzu haka an samu bullar masifar zazzabin cizon soro a tsakanin jama’ar lardin baya ga daruruwan mutane da suka kamu da muggan cututtuka da suke gargarar mutuwa sakamakon rashin magunguna, sannan wasu jama’a da dama da suka samu raunuka a sanadiyyar hare-haren jiragen saman yakin mahukuntan Saudiyya kuma suke bukatar karin jini suna nan kara zube babu magunguna ko jinin da za a kara musu domin samun lafiya.
Har ila yau kungiyar bada agaji ta kasa da kasa ta Hilal-Ahmar ta sanar da dakatar da duk wani aikin jin kai a lardin na taiz sakamakon ci gaba da kai hare-haren ta’addancin mahukuntan Saudiyya da kawayenta duk da cewar akwai daruruwan mutane da suke bukatar agajin gaggawa a yankuna daban daban na lardin.
Mahukuntan Saudiyya da masu goya mata baya daga cikin kasashen Larabawa da kuma Amurka sun fara kaddamar da hare-haren wuce gona da iri ne kan kasar Yeman tun a watan Maris na wannan shekara bisa da’awar dawo da shugaban kasar mai murabus Abdur-Rabbuh Mansur Hadi kan karagar shugabancin Yeman, inda ya zuwa yanzu hare-haren suka lashe rayukan dubban mutane tare da jikkata wasu dubban daruruwa na daban.
A kowace shekara kimanin mutane miliyon 3 ne suke safke farali daga kasashe 180 na duniya, ana saka jami’an tsaro dub 120, da ‘yan sanda dubu 16 da kamarori dubu 30 a lokacin aikin hajji.
3361188