IQNA

Za A Gudanar Da Gasar Kur’ani Mai Tsarki Karo Na 10 A Kasar Rasha

21:48 - September 12, 2015
Lambar Labari: 3361732
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki a birnin Mosco na kasar Rasha.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Karakas Hall cewa, a ranar sha tara ga watan mehr ne za a fara gudanar da gasar a babban dakin taro na Karakas City Hall.

Wannan gasa ta birnin Moscow dai ana gudanar da ita tsawon shekaru goma sha shida tare da halaratr makaranta da mahardata daga kasashen msuulmi da ma wadanda bana musulmi ba.

Masu halartar gasar dai suna suna gudanar da ita  abangarori na harda kur’ani da kuma karatu, gami da kula da kaidojin karatun da kuma mai karatu yake kiyaye su.

Musulmin kasar Rasha sun kai kimanin kashi 20 cikin daro daga yawan mutanen kasar kasar Rasha da suka kai kimanin miliyan 145, kuma suna gudanar da harkokinsu lami lafiya.

3361374

Abubuwan Da Ya Shafa: moscow
captcha