IQNA

An Kammala Bincike Kan Faduwar Nau’urar Daukar Kaya A Haramin Makka

23:50 - September 14, 2015
Lambar Labari: 3362570
Bangaren kasa da kasa, an kammala wani bincike da ake gudanarwa dangane da faduwar na’urar daukar kaya masu nauyi a haramin Makka mai tsarki.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alkhaleejaffairs.org cewa,  idan an kammala aikin kwamitin za a mika rahoton ga sarkin yankin Makka Khalid Faisal Bin Abdulaziz domin yin dubi a kansa.



Rahotanni daga Saudiya na cewa maniyyata da dama ne suka riga mu gidan gaskia, kana wasu kuma suka jikkata sanadin fadowar wani karfen injin lodin kayan gini a masalacin Ka’aba ko Harami a Makka.



Kawo yanzu babu cikaken bayani daga mahukuntan kasar kana bin da rahoton ya kunsa  amman hotunan dake yawo a kafofin yada  labarai na intanet sun nuno  mutane da dama a cikin jinni, a inda karfen ya fado ya kuma rasa har zuwa cikin Harami.



Wasu bayanai na daban sun ce an samu sabkar ruwan sama mai karfi a lokacin da hadarin ya faru. Wannan hadarin dai na zuwa a ‘yan kwananki kalilan kafin gudanarda aikin hajin bana, a daidai lokacinda mahukuntan na Makka ke gudanarda aikin fadada masalacin zuwa metre dubu hudu ta yadda zai iya karbar maniyyata  da dama.



Yawan mutanen da suka rasa rayukansu a haramin Makkah sun haura zuwa 111 sakamakon fadowar karfen da ke lodin kayayyakin gine-gine a ranar Juma’a.

Mahukuntan Saudiyya a safiyar yau Asabar sun sanar da cewa yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon fadowar karfen da ke lodin kayayyakin gine-gine a kan rufin haramin Makkah sun haura zuwa dari da bakawai tare da jikkatan wasu fiye da dari biyu.

Majiyar watsa labaran Saudiyya ta sanar da cewar sakamakon ruwan sama da matsananciyar iska da ke kadawa a birnin Makkah a jiya Juma’a sun yi sanadiyyar gurbatar yana yi tare da karya bishiyoyi gami da fadowar dogon karfen da ke lodin manyan kayayyakin gine-gine a kan rufin haramin Makkah.

Wannan lamarin ya yi sanadiyyar rubzawarsa a kan mutane da suke gudanar da ayyukan ibadu a cikin haramin, kuma ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane da dama maniyyata.

3362246

Abubuwan Da Ya Shafa: makka
captcha