Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Arab News cewa, Bandar Bin Muhammad Hejar ne shugaba hukumar kula da ayyukan hajji ya sanar da hakan, inda ya ce a cikin shekaru 30 masu adadin alhazai kai miliyan 30.
Ya ce a cikin shekaru masu za a mayar da tsarin karbar visa ta hanyar tsari na yanar gizo wato internet ga baki daya, ta yadda kowa zai iya samu ta hanya mafi sauki.
Mahukuntan na kasar Saudiyya sun sanar da cewa za akara yawan mahajjantan ne yan kwanaki bayan faduwar naurar daukar kaya a cikin harami mai tsarki tare d akashe wani adadi mai yawa da kuma jikkata wasu daga cikin masu aikin hajji a bana.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun irin wadannan matsaloli a lokacin gudanar da aikin hajji ba, akan ne ma wasu ke ganin ya kamata a gudanar sauye-sauye kan lamarin kula da hajji ya zama ahannun kasashen muuslmi ne baki daya.
3363021