IQNA

Kur’ani Ya Yi Umarni Da Yin Kyawawan Ayyuka A Cikin Rayuwa

20:54 - September 23, 2015
Lambar Labari: 3366900
Bangaren kasa da kasa, a lokacin bude babban masallacin Morcow a yau shugaban kasar Rasha ya bayyana cewa kur’ani ya yi umarni da aikata kyawawan ayyuka a cikin rayuwa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na news.am cewa, Vladimir Putin shugaban kasar Rasha a lokacin bude babban masallacin Moscow a yau ya yi ishara da ayar kur’ani da ke yin kira zuwa ga aikata alkhairi a surat Ma’idah.48.

Vladimir Pution ya bayyana matsayin musulmin kasar da cewa na asasi ne, kma a kowane lokaci musulmi suna a kan gaba wajen taka gagarumar rawa a cikin dukkanin lamurra na ci gaban al’umma.

Bayan gudanar da karatun kr’ani mai tsarki a lokacin taron bude masallacin, shugaba Putin ya bayyana cewa, a kowane lokaci musulmin kasarsa suna da matsayi na musamamn a cikin dukkanin lamurran kasar, wanda hakan kuma ya samo asali ne tun daga tarihin kasar.

Dangane da masallatan da ke kasar kuwa ya bayyana cewa akwai masallatai masu tarin yawa a sassa na kasar Rasha, amma bude wannan babban masallaci a yau ya sanya shi ya zama shi ne mafi girmaa cikin dukkanin masallatan kasar.

An kwashe tsawon shekaru kimanin 10 ana gina wannan masallaci mafi girma a nahiyar turai baki daya, tare da halartar baki daga sassa na kasa da kuma kasashen ketare, da suka hada da malamai da kuma masana daga kasashen musulmi da sauran da suka hada da jamhuriyar musulunci ta Iran.

Girman masallacin na Moscow ya kai mitane dubu 18 da 900 murabba’i, haka nan kuma zai dauki masallata fiye da dudu 10.

Wanann masallaci yana da hawa shida, kuma akwai hasumiyoyi da kuma tuluwa bakwai, tsawon kowace hasumiya mita 72, tsawon tulluwa kuwa mita 46 ne.

3366859

Abubuwan Da Ya Shafa: rasha
captcha