Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na Bawabah News cewa, Benyamin Netanyahu a cikin yan kawanaki da suka gabata ya halarci wani zaman taro na cika shekar 65 da kafa kungiyar liken asirin MOSSAD ta haramtacciyar kasar Isra’ila da ke kusa da birnin Tel Aviv.
Ya ce musulmi da suka hada da sunna da Shi’a duk sun yi imanin cewa Isra’ila ba ta wurin zama a cikin duniya musulmi, sun hadu a kan hakan ba tare da wani banbanbci ba.
Netanyahu y ace amfanin Isra’ila ne a ci gaba da rikicin da ake fama da shi a yanzu a cikin kasashen larabawa.
Ya kara da cewa duk da cwwa wasu daga cikin larabawa suna goyon bayan Isra’ila dari bisa dari a cikin dukkanin abin take yi, amma kungiyar Mossad za ta kasance wata babbar cibiyar da zata kare samwarsu a nan gaba.
3372713