Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ippmedia cewa, Musulmin kasar Tanzania sun bukaci da a gudanar da bincike dangane da abin da ya faru a aikin hajjin bana musamman ma a ranar idin layya a lokacin jifar shedan, inda dubban mutane suka rasa rayukansu.
Haka nan kuma ya bayar da rahoto daga birnin Daru salam an kasar Tanzania cewa, babbar majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Tanzania da ma wasu daga cikin kungiyoyin musulmi na kasar sun mika takardu gwamnatin kasar, da ke yin kira da a bi kadun abin da ya faru da alhazan kasar a Saudiyya.
Sheikh Abdulkarim Almas daya daga cikin manyan malamai na kasar kuma mamba a kwamitin zartarwa na majalisar malaman kasar ya bayyana cewa, abin da ya faru ba a bu ne da ya kamata ya wuce haka nan ba tare da bincike ba, kuma bai kamata ya zama bangare daya ne zai gudanar da binciken ba, ya ce ya kamata ne a kafa kwamiti na kasashen musulmi da za su gudanar da bincike kan hakinanin abin da ya faru.
Dangane da dora alhakin abin da ya faru kan alhazan Afirka da mahukuntan Saudiyya suka yi a farkon lamarin, Sheikh Abdulkarim ya nuna takaicinsa matuka dangane da hakan, inda ya ce shi a gabansa komai ya faru, kuma yana da abubuwa da zai fada musamamn kan batun rufe musu kofofi da askarawan gwamnatin Saudiyya suka yi a lokacin jifar shedan, wanda shi ne masomin farin matsalar da ta faru a Mina.
Da dama daga cikin al’ummomin kasashen duniya dai suna ci gaba da nuna rashina mincewarsu da abin da abin da ya faru, tare da matsa lamba ga gwamnatocinsu domin a gudanar da bincke kan makomar alhazan kasashensu.
3377890