Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Sabrina Razzaq Hussai marubuciya ‘yar kasar Birtaniya ta rubuta ajaridar Guardian cewa, akwai dalilai da suka jawo mutuwar alhazai a Mina da suke da alaka da rashin kulawa ta mahukuntan saudiyya kai tsaye.
Hakika rashin cancantar daukar dawainiyar gudanar da ayyukan hajji da matakin sakaci da ko-in kula gami da rashin aiki da hakkin da ya rataya a kan mahukuntan Saudiyya sune musabbabin faruwar hatsarin Mina da ya kai ga hasarar dubban rayukan mahajjata aikin hajjin bana da suka fito daga sassa daban daban na duniya.
Bayan shudewar kwanaki shida da faruwar hatsarin Mina, dalilai da hujjoji da suke tabbatar da sakaci, halin ko in kula da rashin aiki da hakkin da ya rataya a wuyar mahukuntan Saudiyya wajen gudanar da ayyukan hajji suna kara bayyana a fili duk da matakan farafaganda da yada labarun karya marassa tushe da mahukuntan Saudiyya da 'yan korensu ke yi a sassa daban daban na duniya.
A matakin farko, gidan sarautar Saudiyya ya yi kokarin rufe matsalar hatsarin Mina tare da bayyana cewa wata karamar matsala ce da ta saba aukuwa a lokacin aikin hajji ta turereniya da rashin hakurin mahajjata amma bayan da yawan mahajjatan da suka rasa rayukansu yake ci gaba da karuwa, hakan ya tilastawa mahukuntan Saudiyya canza baki tare da daukan matakin boye hakikanin abin da ya janyo hatsarin musamman ganin yadda kasashen musulmi suka fito fili suna bayyana tsananin damuwarsu kan batun.