IQNA

An Bude Babbr Cibiyar Muslnci Ta Ahlul Bait (AS) A kasar Cheque

22:45 - October 10, 2015
Lambar Labari: 3383831
Bangaren kasa da kasa, an bde wannan babbar cibiyar Ahlul bait (AS) ne a birnin Berno na kasar ta Cheque tare da halartar wakilin Ayatollah Sayyid Ali Sistani.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa nanyanar gizo na iraaqi.com cewa, Allamah Sayyid Murtadha Keshmiri wakilin Ayatollah Sayyid Ali Sistani shi ne ya jagoranci bude wannan babbar cibiyar mulsunci ta Ahlul Bait (AS).

A lokacin da yake gabatar jawabinsa, ya bayyana cewa babbar manufar bude cibiyar dai it ace kara fitoda ilmi da kuma koyarwarr iyalkan gidan manzo Ahlul bait (AS) ga al’ummomi na wannan yanki.

Keshmiri y ace wannan cibiya tana  amatsayin wani bangare ne na cibiyar Imam Ali (AS) da ke birnin London.

Ya ci gaba da cewa bude wannan cibiya zai taimaka matuka wajen kara isar da sakon iyaln gidan amnzon Allah ga mabiya addinin muslunci da suke zane a wannan kasa da ma wasu kasashen da ksa, kamar yadda wadanda ba msulmi ba za su amfana matuka wajen kara sanin addinin muslunci.

An samu halartar wasu daga cikin jami’an ofisoshin jakadancin wasu daga cikin kasashen larabawa a wajen taron taron bude cibiyar, kamar yadda kuma wasu daga cikin jami’a na kasar sun samu halarta a hukumance.

Walid Ha,id Shatagh mataimakin jakadan kasar Iraki a wannan kasa ya samu halartar wurin, kuma ya gabatar da jawabi da ke jan hankula matuka wajen mayar da hankali koyarwarwa ta iyalan gidan manzon Allah (AS) a cikin dukkanin lamurra na rayuwa.

Kamar yadda kuma Haj Abdulrahman Hammud fitaccen makarancin kur’ani mai tsariki ya gabtar da karatun alkur’ani mai tsarki na wasu ayoyi masu albarka a wurin, dominsamun albarkacin kur’ani mai tsarki a wannan cibiya.

3383469

Abubuwan Da Ya Shafa: Ahlul Bait (AS)
captcha