IQNA

Daesh Na Bayar Da Makudan Kudade Ga Masu Tura Mata Mayaka ‘Yan Ta’adda

23:06 - October 17, 2015
Lambar Labari: 3386752
Bangaren kasa da kasa, masana sun ce ‘yan ta’addan Daesh na kashe makudan kudade domin samun masu taya su a yauuakan ta’addanci inda suka bayar da kudi da suka kai dala dubu 10 ga duk dan ta’adda guda.


Kamfain dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na (The Asian Age) cewa, A lokacin da shugabar kwamitin Elizabetha Cariska take gabara wa Majalisar dinkin duniya da rahoto a jiya Juma’a kan sakamakon binciken da suka gudanar a kasar Belgium kan wannan lamari, ta bayyana cewa kungiyar Daesh tana biyan kudade ga mutanen da suke samo musu mayaka da suka kai dalar Amurka dubu 10 a kan kowane mutum daya.

Ta ce akwai wata kungiya ta kunshi wasu masu tsatsauran ra’ayi ta tura mutane da dama daga kasar ta Belgium zuwa Syria da Iraki tun a cikin shekara ta dubu biyu da goma, da suka hada da mata da maza, wadanda akasarinsu larabawa ne.

Masu turawa da mayaka zuwa Syria sun canja hanyar yin hakan, inda suke amfani da hanyoyin sadarwa na zamani, inda suke samun irin mutanen da suke bukata domin tura su Syria da Iraki, kuma suna karbar kudade aga daga dubu 2 har zuwa dala dubu 10 a kan kowane mutum daya, amma idan mutumin yana da wata kwarewa ta musamman, kamar likita, ko injiniya, kudin da suke karba a kansa suna yawan gaske.

Cariska ta ce ya zuwa yanzu dai akwai mutane daga Belgium da suke yaki a sahun ‘yan ta’adda na ISIS a Syria ko Iraki da yawansu ya kai 500, inda maza daga cikinsu ke yin yaki, mata kuma sukan yi ayyukan jinya da kuma auren maza da ke  yaki a cikin sahun ‘ya’yan kungiyar.

Wannan kwamiti dai ya fara gudanar da aikinsa ne a kasar unisia, kasa ta biyu wajen yawan ‘yan ta’addan ISIS da suke yaki a Syria da Iraki bayan Saudiyyah, inda  a can hanyoyin da masu tura ‘yan ta’addan suke bi sun kama da na takwarorinsu na Beilgium, duk kuwa da cewa sauyin gwamnatin da aka samu bayan kayar da jam’iyyar nehdah a zaben ‘yan majalisa, ya dakushe harkar aikewa da ‘yan ta’adda zuwa kasashen Syria da Iraki.

3386643

Abubuwan Da Ya Shafa: isis
captcha