A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Iqna Professor Sashedina malami a jami’ar Virginia ta kasar Amurka ya bayyana babban tasirin mikewar Ashura akan wasu manyan fitattun mutane na duniya.
Professor Sashedina ya ci gaba da cewa akwai laurra da dama da suka faru a duniya da suke da matukar muhimmanci wadanda kma suke da alaka da darussan da aka dauka daga wakliar Ashura, daya daga cikinsu kuwa shi ne gwagwarmayar da aka yi da turawan Birtaniya a India.
Ya ce wanda ya jagoranci wannan gwagwarmaya ta neman yanci daga mulkin mallakar turawan Birtaniya Mahatima Gandi ya bayyana abin da Imam Hussain (AS) ya yin a sadauukantarwa da rashin mika wuya ga azzalumai a matsayin babban darasi abin koyi a rayuwarsa.
Tasirin wannan lamari ya kara zaburar da Gandi wajen ci gaba da fafatawa tare da yan mulkin mallaka, duk kuwa da irin cutarwar da suka yi masa da jama’arsa d suke kan tafarkinsa na neman yanci, hakan bai sanya sun yi rauni ba, domin kuwa sun dauki darasi ne daga sadaukatarwa Imam Hussain (AS) a ranar Ashura.
Ko shakka babu abin da Imam Hussain (AS) ya yi shi ne babban abin da ya kamata ya zama darasi ga dukkanin al’ummomin duniya da suke son su rayu a cikin yanci, tare da zama masu bin abin da suka yi Imani da shi a cikin yanci, ko kuma su rasa rayukansu a kan hakan, wanda kuma shi ne nasara ta karshe, ka rabu da duniya kana kana bin da ka yi iamni da shi.
Na’abucin matsayi mai girma Imam Hussain (AS) ya sadaukantar da rayuwarsa domin tseratar da al’umma daga duhun zalunci da danni da babakere a kan tunai da imanin mutane, wanda sadaukantawras ta zama ma’aunia bayansa na tantance haske da duhu gaskiya da karaya, adalci da zalunci, wanda kuma hakan ya tabbatar da nasarar gwagwarmayarsa har zuwa karshen duniya.
3389063