IQNA

An Gudanar Da Sallar Zuhur Ta Ranar Ashura A Kasar Malayzia

19:17 - October 24, 2015
Lambar Labari: 3393129
Bangaren kasa da kasa, mabiya tafarkin shi’a daga birnin Kualalmpour fadar mulkin kasar Malayzia mai tazarar kilo mita dubu 6 da 800 zuwa Karbala sun gudanar da sallar zuhur domin tunawa da ranar Ashura.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Shafaqna cewa, daruruwan mabiya tafarkin shi’a daga birnin Kualalmpour sun gudanar da sallar zuhur domin tunawa da ranar Ashura da kuam shahadar Imam Hussain (AS)

Bayanin ya ci gaba da cewa wadanda suka halarci wannan zaman sun jaddada azamarsu ta ci gaba da bin tafarkin manzon Allah da iyalan gidansa tsarkaka da kuma tunawa da zaluncin da aka yi Imam Hussain (AS) da sauran dukkanin limaman shiriya na gidan manzo.

An gabatar da jawabai da kuma juyai na shahadar Imam Imam Hussain (AS) inda Hojjatol Islam Mahmud Marvi ya rika kiran sunan Zainab (SA) da kuma Imam Hussain (AS) inda mutane da ke wurin suka barke da kuka domin juyayin abin da ya samu wadannan bayin Allah a irin wannan rana ta Ashura.

A nasu bangaren Iraniyawa mazauna kasar Malayzia  biranan Sardang, Juhur, Pinang duk sun gudsanar da wannan taro na mai albarka.

3393038

Abubuwan Da Ya Shafa: ashura
captcha