Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al’ahd cewa, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid hassan Nasrullah ya halarci babban taron ranar Ashura a birnin Beirut.
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyeed Hassan Nasurullah ya halarci taron Ashoora a birnin Berut a safiyar yau Asabar inda ya yi jawabi na wasu dakikoki a karshen taron.
Da farko Sayyeed Nasarallah ya mika ta’aziyyasa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci a nan Iran Aya. Sayyeed Aliyun Khaminaee da kuma sauran maraji’ai da musulmai kan juyayin shahadar Imam Husain(as).
Sayyees nasarallag ya kara jaddada goyon bayan kungiyarsa ga gwagwarmayan da Palasdinawa suke yi da yahudawan haramtacciyar kasar Isra’ila sannan ya kara da cewa kungiya zata ci gaba da mallakar makamai wadanda zata yaki da kuma yan ta’adda masu kafirta musulmi da su.
Dangane da kasar Iraqi kuma Sayyeed Nasarallah ya ce kada su dogara da Kasar Amurka don yakar kungiyar Daeesh, su dogara da kawukansu kadai kan wannan wajibin, za su kuma sami nasara da yardar Allah
Nasarallah ya yi Allah wadai da mahukuntan kasar Saudia kan ta’asan da sike aiwatarwa a kasashen Yemen Bahrain da kuma Syria, sannan ya bukaci a yi bincike kan dalilin da suka haddasa mutuwar mahajjata a Mina a cikin hajjin wannan shekara.
Daga karshe dangane da siyasar kasar Lebanon kuma S. Nasarallah ya bukaci kungiyoyin siyasar kasar su shiga tattaunawa tsakaninsu da gaskiya kada su jira wasu kasashen yankin su fada masu abinda zasu yi.