IQNA

Fiye Da Mutane Miliyan 6 Ne Suka Halarci Tarukan Ashura A Bana A Karbala

21:36 - October 25, 2015
Lambar Labari: 3393616
Bangaren kasa da kasa, Nasif Al-khitabi shugaban majalisar lardin Karbala ya bayyana cewa an gudanar da tarukan Ashura a cikin nasara tare da halarar mutane miliyan 6 da dubu 300.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo na Saumaria News cewa, Nasif Al-khitabi a taron manema labarai ya bayyana  cewa an gudanar da tarukan Ashura a cikin nasara tare da halarar mutane miliyan 6 da dubu 300 da suka halarci hubbarori masu tsarki.

Ya ci gaba da cewa an gudanar da wadannan taruka masu alabarka  acikin nasara ba tare da fuskantar wata matsala ta tsaro ba, kuma wanann shi ne karon farko da aka yi amfani da jiragen F-16 wajen kare masu ziyarar.

Nasif ya ce mutane dubu 300 sun zo kasar iraki ne daga kasashen duniya 26 domin halartar wadannan taruka masu albarka a birnin na karbala mai alfarma.

Ya ce duk da irin matsaloli na tattalin arziki da ake fama da su a tsakanin mutane a birnin an karbala, amma a n gudanar da tarukan cikin nasara, tare da taimakon kungiyoyi masu taimakawa kimanin 560 daga sassa na kasar ta Iraki da kewaye.

Mahukuntan lardin Karbala sun bayyana cewa a ranar da aka gudanar da sassarfar Turaij, kimanin mutane miliyan 3 suka halarci wurin, yayin da kuma a bangaren jami’an tsaro, an jibkge kimanin dubu 30 domin bayar da kariya ga masu aikin na ibada.

3393204

Abubuwan Da Ya Shafa: ashura
captcha