Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «vetogat» cewa, za a gudanar da wannan taroi ne tare da halartar Yasmin Alhusri diyar fitacce makarancin kur’ani mai tsarki Sheikh Khalil Alhusri dan kasar Masar domin tunawa da ayyukansa na kur’ani mai tsarki.
Wannan aiki na kafa wannan babban kwalejin ilmomin kur’ani mai tsarki yana da alaka ne da cibiyar Azahar a reshenta na Bani mazar,a cikin gundumar Bihinsa da ke cikin kasar ta Masar, kum,a hakan zai zama daya daga cikin ayyukan da aka yi mafi muhimmanci domin tunawa da shi da ayyuan alkhairi da ya gudanar a bangaren kur’ani.
Umar Abdulkafi daya daga cikin masu aikin isar da sako, da kuma Mahmud Abdulhafiz wakilin cibiyar Azhar, duk sun halarci wurin kaddamar da wannan shiri, wanda zai bayar da damar dora harsashin gina wannan babbar cibiyar.
3394869