IQNA

Wani Malami A Palastinu Ya Tarjama Kur’ani A Cikin harshen Hebru

23:16 - October 26, 2015
Lambar Labari: 3395065
Bangaren kasa da kasa, Sobhi Adwa wani malami mai karantar da yara kur’ani mai tsarki a palastinu ya tarjama kur’ani mai tsarkia cikin harshen Hebru.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aljazeera cewa, Sobhi Adwa daga kauyen Tar’an a cikin nasirah wani malami mai karantar da yara kur’ani mai tsarki a palastinu ya tarjama kur’ani mai tsarkia  cikin harshen Hebru domin amfanin masu fahimtar yaren.

Wannan tarjama ta samu dubuwa da tantancewa daga Zaidul Ais babban daraktan cibiyar Bayanat da ke birnin Amman na kasar Jordan, inda aka kwashe kimanin kwanaki 1000 ana duba wannan tarjama kafin tabbatar da ita.

Zaidul Ais ya ce babbar manufar tantance wannan tarjama it ace tabbatar da cewa an isar da sakon muslunci ga yahudawa da bas u da wata masaniya kan wannan addini mai tsarki.

Ya ci gaba da cewa ko shakka babu wannan aiki zai zama mai tasiri matuka ga yahudawan da suke son su san wani abu dangan eda addinin da kuma abin da yake koyar da musulmi, domin kuwa ba dukkaninsu ba ne suka taru suka zama.

Wanann tarjama dai ta bayar da muhimmanci matuka wajen bayyana ma’anar ayoyin kr’ani da yan tacciyar tarjama, ta yadda mai fahimtar yaren zai gane abin da ake Magana a knasa saboda saukin tarjamar, maimakon yin amfani da kalmomi masu wahala.

Aikin dai ya samu karbuwa daga palastinawa tare da bayyana shi babban abin alfahari ga mtumin da ya kwwashe shekaru fiye da 40 yana koyar da kur’ani mai tsarki ga palastinawa mazauna kauyen Tauan.

Sheikh Muhammad dahamisha limamin masallacin Abubakar ya bayyana wannan aikin tarjama da cewa, wani sako na muslunci zuwa ga yahdawa.

3393286

Abubuwan Da Ya Shafa: Palestinu
captcha