IQNA

Zartar Da Hukuncin Kisa Kan Sheikh Nimr Yana Matsayin Kunna Wutar Fitina

22:14 - October 28, 2015
Lambar Labari: 3407230
Bangaren kasa da kasa, kawancen malaman gwagwarmaya na kasashen duniya ya fitar da wani jawabi da a cikinsa ya gargadi kasar Saudiyya kan zartar da hukuncin kisa kan Sheikh Nimr tare da bayyana hakan a matsayin kunna wutar fitina.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Al-ahd News cewa, kawancen malaman gwagwarmaya na duniya ya fitar da bayanin gargadi gargadi ga kasar Saudiyya kan zartar da hukuncin kisa kan Sheikh Nimr.
Bayanin y ace daukar duk wani mataki mai da hakan yana da matukar hadari ga ita kanta kasar Saudiyya da mahkntanta, domin hakan zai kawo tashin hankali da rshin zaman lafiya a kasar da wata kila ma ya shafi wasu kasashen na daban, kuma Saudiyya it ace silar hakan.
A nasa bangare shugaban kwamitin tsaro da harkokin kasashen waje na majalisar shawarar Musulunci ya ja kunnen gwamnatin Saudiyya cewa zartar da hukuncin kisa a kan daya daga cikin manyan malaman Shi’a na kasar Sheikh Nimr Baqir al-Nimr za ta haifar da sabon rikici a yankunan da ‘yan Shi’a suka fi yawa a kasar da wahabiya ke mulki.
Ya bayyana hakan ne a  yau din inda ya ce zartar da hukuncin kisar da aka yanke wa Sheik al-Nimr zai haifar da gagarumin rikici a yankunan ‘yan Shi’an wanda ko shakka babu hakan ba zai yi kyau ga gwamnatin ta Saudiyya ba, don kuwa babu abin da Shehin malamin yayi face wa’azi da Magana da kuma kin zaluncin mahkunta.
Duk kuwa da cewa dai wannan dai ba shi ne karon farko da jami’an Iran daban-daban suka ja kunnen Saudiyyan kan aiwatar da wannan hukuncin ba, don bayan da aka tabbatar da shi a jiya.
Shi ma a nasu bangare al’ummar Saudiyya da suke gabashin kasar suna ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayansu ga Sheikh Nimr Baqir Nimr da mahukuntan kasar suka yanke masa hukuncin kisa.
Tun daga daren Alhamis yau dare uku a jere ke nan al’ummar garin qatif da ke gabashin Saudiyya suke gudanar da zanga-zangar jaddada goyon bayansu ga sheikh Nimr Baqir Nimr malamin ‘yan shi’a da ke gwagwarmayar neman ‘yanci daga bakar siyasar zalunci da babakeren gidan Saurautar kasar.
Masu zanga-zangar suna rera taken yin gargadi ga mahukuntan kasar ta Saudiyya kan nisantar zartar da hukuncin kisa kan Sheikh Nimr Baqir Nimr tare da hanzarta sakinsa.
Tun dai wata kotu a kasar ta Saudiyya ta yanke hukuncin kisa kan sheikhin malamin saboda shahararsa a fagen yaki da nuna bambanci a tsakanin ‘yan kasar tare da neman aiwatar da tsarin dimokaradiyya da zai kawo karshen babakere mahukuntan kasar.

 

3402831

Abubuwan Da Ya Shafa: Nimr
captcha