IQNA

Ban Ki Moon Ya Kirayi Masarautar Saudiyya Ta Janye Batun Kisan Sheikh Nimr

23:11 - October 29, 2015
Lambar Labari: 3412380
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren majalisar dinkin duniya ya kirayi mahukuntan kasar saudiyya da su gagaguta janye batun kisan suke shirin yi kan Sheikh Nimr.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-sabil cewa, Steven Dojarik kakakin bababn sakataren majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa, Ban Ki Moon ya kirayi sarki Salman na Saudiyya da su gagaguta dakatar da batun kisan suke shirin yi kan Sheikh Nimr babban malamin Shi’a a Saudiyyah.

Wani adadi mai yawa na ‘yan kasar Saudiyya da masu goya musu baya sun gudanar da wata zanga-zanga a ofishin jakadancin kasar da ke birnin London don nuna rashin amincewarsu da ci gaba da tsarewa da kuma azabtar da ‘yan adawa da gwamnatin kasar take yi.

Rahotanni daga birnin London din sun ce masu zanga-zangar dai suna Allah wadai ne da abin da suka kira mulkin kama-karya da kuma ci gaba da tsare masu adawa da mulkin mulukiyya na Saudiyyan.

Masu zanga-zangar har ila yau sun yi Allah wadai da ci gaba da tsare babban malamin Shi’a na kasar Sheikh Nimr Baqir al-Nimr da gwamnatin Saudiyyan take ci gaba da yi suna masu zargin gwamnatin da kirkirar karya kansa da kuma hana shi samun kulawa ta likitanci.

Kungiyoyin kare hakkokin bil’adama  na kasa da kasa da dama suna ci gaba da sukar kasar Saudiyyan saboda take hakkokin al’ummar kasar da take ci gaba da yi.



3409311

Abubuwan Da Ya Shafa: Moon
captcha