Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Magrib Youm cewa, Ahmad Alumran masani kan lamurran kur’ani kuma mamaba a kwamitin kula da harkokin ilimi ya bayyana cewa adadin mahardata kur’ani mai tsarki a Morocco ya kai miliyan 1.1 a kasar a halin yanzu.
Ya ce a kowace adadin mahardata kur’ani yana karuwa akasar da dubban mutane, yayin da ake ta gasa wajen shiga bangarori na kwarewa kan lamrra da suka shafi kur’ani mai tsarki.
Ahmad Alumran ya kara da cewa, wannan lamari ya faru ne sakamakon kirlkiro da wani bangare tadabbur kan ayoyin kur’ani mai tsarkia kasar, wanda hakan ya sanya mutane suke ta kara bayar da himma kan lamarin kur’ani, kuma ana san zai kara samun magoya baya.
Alumrani ya gabatar da jawabi a makon da ya gabata a wajen taron tadabbur na kasa da kasa da aka gudanar a kasar.
3442104